Shugaban Hukumar Alhazai ta Kasa (NAHCON), Ambasada Isma’il Abba Yusuf, ya bayyana cewa bin jadawalin shirye-shiryen aikin Hajji abu ne da ba za a yi sassauci a kansa ba, yana mai cewa hakan ne ginshiƙin ingantaccen tsari da gudanar da aikin Hajji cikin nasara.
Shugaban NAHCON ya bayyana haka ne a wata hira da ya yi da manema labarai yayin ziyararsa a Jihar Nasarawa.
Ya ce a tsawon shekaru, Najeriya ta fuskanci matsalar rashin bin jadawalin aikin Hajji yadda ya kamata, yana mai jaddada cewa hukumar ta kuduri aniyar tabbatar da cikakken bin jadawalin da hukumomin Saudiyya suka tsara.
A cewarsa, “Jadawalin aikin Hajji abu ne mai muhimmanci kuma ba abin wasa ba ne domin an tsara shi ne bisa tsari na kalanda.
Daya daga cikin manyan matsalolin da muka dade muna fuskanta a Najeriya shi ne rashin bin jadawalin da aka tsara. A wannan karon, mun kuduri aniyar bin jadawalin da Saudiyya ta tsara ba tare da kauce masa ba.”
Ambasada Isma’il Abba Yusuf ya bayyana cewa an tsara jadawalin ne domin sauƙaƙa shirye-shiryen da Masarautar Saudiyya ke yi kafin aikin Hajji, kasancewar tana karɓar kusan mahajjata miliyan biyu daga sassa daban-daban na duniya a kowace shekara.
Ya ce kafin fara aikin Hajji, hukumomin Saudiyya kan gudanar da manyan shirye-shirye da suka haɗa da samar da ingantattun ayyukan kiwon lafiya, ababen inganta rayuwa, ruwa, wutar lantarki, masauki da kuma hanyoyin sufuri domin tabbatar da jin daɗin mahajjata.
Ya ƙara da cewa cikakken bin jadawalin aikin Hajji zai bai wa Najeriya da Saudiyya damar kammala dukkan shirye-shiryen da suka dace a kan lokaci, tare da tabbatar da gudanar da aikin Hajji cikin tsari da inganci ga mahajjatan Najeriya.

