Hukumar Kula da Birnin Makkah da Wuraren Masu Tsarki ta yi amfani da fasahar taswirar ƙasa (Geospatial Technology) da tsarin nazarin bayanai (Business Intelligence) domin inganta gudanar da aikin Hajjin shekarar 1447 Hijira (2026), ta hanyar sa ido kan zirga-zirgar alhazai, hanyoyi da kuma ayyukan hidima a wuraren aikin Hajji.
Hukumar ta bayyana cewa ta sarrafa bayanan sama da wurare, alamomi da cibiyoyin hidima 20,000, waɗanda aka haɗa cikin taswirori na dijital sama da 20 da suka shafi Wuraren Masu Tsarki, tsakiyar birnin Makkah da kuma Masallacin Harami.
Ofishin Kula da Bayanai na Hukumar ya haɗa waɗannan bayanai da hukumomin gwamnati 30, lamarin da ya ba da damar bibiyar yadda ake gudanar da ayyuka a lokaci na ainihi tare da inganta haɗin gwiwa tsakanin hukumomin da ke yi wa alhazai hidima.
Ta hanyar tsarin taswira na Hudhud, ƙungiyoyin aiki sun sarrafa bayanan wurare sama da 4,400, sun sabunta sassan hanyoyi fiye da 3,250 tare da yin rajistar rufe hanyoyi 70. Ana sabunta duk wani canji cikin ƙasa da daƙiƙa 60 domin masu gudanar da ayyukan Hajji su samu bayanai cikin gaggawa.
Haka kuma, tsarin taswira na Baladi ya tantance muhimman wurare 8,248 masu alaƙa da aikin Hajji, sannan ya ƙara sabbin wurare 3,119 a Wuraren Masu Tsarki domin sauƙaƙa wa alhazai gano wurare da kuma samun hidimomi.
A fannin kula da zirga-zirga kuwa, Hukumar ta yi amfani da wani dandali na lura da yanayin hanyoyi da cunkoson jama’a, inda aka sarrafa hotunan zirga-zirga miliyan tara tare da nazarin bayanan wurare sama da 350,000.
Tsarin ya rufe hanyoyi masu tsawon fiye da kilomita 1,400, sannan ya haɗa tashoshin bas 419 da jadawalin zirga-zirgar su kai tsaye.
Alhazai kuma sun amfana da dandalin Digital Spatial Guidance, wanda ya ƙunshi taswirori 11 na jagoranci da ke ɗauke da wurare sama da 5,000 a fannoni daban-daban kamar kiwon lafiya, ilimi, ayyukan addini, sufuri da yawon buɗe ido.
A lokacin Hajjin 1447, an yi amfani da waɗannan taswirori sau 537,197.
Taswirar Masallacin Harami ita ce aka fi amfani da ita sau 233,590, sai taswirar iyakokin birnin Makkah wadda aka yi amfani da ita sau 69,275, sannan taswirar muhimman wurare da sansanonin alhazai wadda ta samu amfani sau 44,084.
Hukumar ta ce za ta ci gaba da sabunta bayanan hanyoyi da wurare, ƙarfafa musayar bayanai tsakanin hukumomi, da kuma inganta taswirori da dandamalin dijital domin ƙara inganta shirye-shiryen gudanar da aikin Hajji a shekaru masu zuwa.
(II)

