An soke kusan jirage 1,500 a manyan filayen jiragen sama guda uku na Saudiyya, biyo bayan wasu hare-hare da aka danganta da ‘yan tawayen Houthi na Yemen, lamarin da ya haifar da tsaiko a harkokin sufurin jiragen sama tare da barin daruruwan matafiya, ciki har da mahajjatan Umrah, cikin mawuyacin hali.
Bayanan bin diddigin zirga-zirgar jiragen sama na Flightradar24 sun nuna cewa an samu rahoton soke jirage 871 a ranar Lahadi, yayin da aka sake soke wasu 614 a ranar Litinin a filayen jiragen sama na King Khalid da ke Riyadh, King Abdulaziz da ke Jeddah, da King Fahd da ke Dammam.
Riyadh ce ta fi fuskantar matsalar, inda aka soke jirage 655 a ranar Lahadi, wato kusan kashi 98 cikin 100 na jiragen da aka shirya tashi. Zuwa safiyar Litinin, an sake soke jirage 436, wanda ya kai kashi 64 cikin 100 na jiragen da aka tsara.
A Jeddah, an soke jirage 158 a ranar Lahadi, sannan aka soke wasu 115 a ranar Litinin. A Dammam kuma, an soke jirage 58 a ranar Lahadi da wasu 63 a ranar Litinin.
Hare-Hare Sun Shafi Filayen Jiragen Sama
Rikicin ya biyo bayan hare-haren da aka kai kan wasu cibiyoyin zirga-zirgar jiragen sama na Saudiyya.
An dakatar da zirga-zirgar jirage na ɗan lokaci a filin jirgin saman King Khalid na Riyadh bayan wani hari da aka kai ranar Asabar, wanda rahotanni suka ce ya kashe akalla mutane 12 tare da jikkata fiye da 300.
A ranar Lahadi kuma, wani hari ya sake afkawa Terminal 4, inda aka ruwaito mutuwar mutum guda tare da jikkata wasu 11, kamar yadda hukumomin kula da zirga-zirgar jiragen sama na Saudiyya suka bayyana.
Haka kuma, an kai hari kan filin jirgin saman King Fahd da ke Dammam a yammacin Lahadi. Hukumomi sun ce ana ci gaba da tantance barnar da aka samu tare da gudanar da binciken tsaro.
Mahajjatan Umrah Na Cikin Wadanda Lamarin Ya Shafa
Mahajjatan Umrah na daga cikin matafiyan da lamarin ya shafa sakamakon soke jirage da tsaikon da aka samu.
Gidan Talabijin na Saudiyya ya nuna hotunan wasu mahajjata a filin jirgin saman Riyadh suna shirin shiga jirgi a lokacin da wani hari ya haddasa fargaba a cikin tashar jirgin.
Ma’aikatar jin daɗin ’yan Bangladesh mazauna ƙasashen waje ta ce kusan ’yan Bangladesh 500 sun makale a Riyadh sakamakon rikicin..
Kamfanonin Jiragen Sama Sun Dakatar da Wasu Jirage
Kamfanonin jiragen sama na ƙasashen duniya da dama sun soke ko dakatar da wasu jiragensu zuwa Saudiyya saboda halin tsaro..
Etihad Airways ta soke wasu jirage tsakanin Abu Dhabi da Riyadh, Jeddah da Dammam, yayin da Emirates ita ma ta soke wasu jirage zuwa wasu biranen Saudiyya.
Kamfanin flydubai ya tsawaita soke jiragen da ke zuwa Riyadh har zuwa ranar 14 ga Oktoba, yayin da Lufthansa Group ta dakatar da jiragen Riyadh har zuwa 16 ga Oktoba.
Wasu kamfanonin jiragen sama na Indiya ma sun soke wasu daga cikin ayyukansu.
A halin da ake ciki, ofishin jakadancin Saudiyya da ke Dubai ya shirya motocin bas domin taimaka wa wasu ’yan Saudiyya da suka makale a Hadaddiyar Daular Larabawa.
Amurka Ta Fitar da Gargadin Tsaro.
Hukumar Kula da Jiragen Sama ta Tarayya ta Amurka (FAA) ta shawarci kamfanonin jiragen sama na Amurka da su yi taka-tsantsan yayin shawagi zuwa ko ta sararin samaniyar Saudiyya.
Hukumar ta bayyana cewa gargadin ya samo asali ne daga ci gaba da ayyukan soji da kuma yiwuwar samun matsala wajen tsarin sadarwa da kewayawa na jiragen sama.
An ce gargadin zai ci gaba da aiki har zuwa ranar 10 ga Disamba.
Yawan soke jiragen ya haifar da gagarumar tangarda a manyan cibiyoyin zirga-zirgar jiragen sama na Saudiyya, musamman Riyadh, yayin da hukumomi ke ci gaba da tantance yanayin tsaro, sannan kamfanonin jiragen sama ke sake tsara jadawalin zirga-zirgarsu.

