Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Sokoto ta yi rijistar jimillar masu niyyar zuwa aikin Hajjin shekarar 2027 guda 2,758, inda ta kammala aikin rijistar da gabatar da bayanan mahajjata bisa wa’adin da Hukumar Kula da Aikin Hajji ta Kasa (NAHCON) ta gindaya.
A sanarwar da Shugaban sashen yada labarai da sadarwa na Hukumar, Faruku Umar ya fitar, Shugaban Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Sokoto, Alhaji Aliyu Musa, ne ya bayyana hakan a yayin wata ganawa tsakanin shugabanci da jami’an Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Sokoto da kuma Mataimakan
Jami’an Rajistar Hajji na Kanana Hukumomin 23 na jihar Sokoto.
Alhaji Aliyu Musa ya yaba wa Mataimakan Jami’an Rajistar Hajji bisa yadda suka dauki mataki cikin gaggawa da kuma jajircewarsu wajen ganin an kammala aikin rijistar cikin wa’adin da aka kayyade.
Ya bayyana cewa kokarin da jami’an suka yi ya taimaka matuka wajen ganin Hukumar ta bi ka’idoji da wa’adin da hukumomin Saudiyya da kuma NAHCON suka gindaya dangane da aikin Hajjin 2027.
Shugaban Hukumar ya kuma bukaci jami’an rajistar da su ci gaba da gudanar da ayyukansu cikin kwarewa, gaskiya, rikon amana da jajircewa, tare da tabbatar da cikakken bin dukkan ka’idoji da matakan da suka shafi aikin Hajji.
SAMA DA MUTANE 3,000 SUN NUNA SHA’AWAR ZUWA HAJJI, YAYIN DA KASON SOKOTO YA TSAYA KAN 2,758
Da yake nasa jawabin a wajen taron, Sakataren Dindindin na Hukumar, Alhaji Ibrahim Umar JJ, ya bayyana cewa sama da mutane 3,000 ne suka nuna sha’awar gudanar da aikin Hajjin 2027 ta Jihar Sokoto.
Sai dai ya bayyana cewa Jihar Sokoto ta samu kujerun Hajji 2,758 ne kawai, wanda hakan ya sa Hukumar ba ta samu damar Rijistar dukkan masu niyyar Hajjin da suka nuna sha’awa ba.
Sakataren Dindindin ya bayyana cewa Hukumar ta yi kokari sau da dama wajen neman karin kujerun Hajji daga NAHCON, amma kokarin bai samu nasarar da ake bukata ba.
Saboda haka, Alhaji Ibrahim Umar JJ ya shawarci masu niyyar zuwa Hajji wadanda suka biya kudin ajiya amma ba su samu kujerar Hajji ba, da su karbi wannan lamari a matsayin kaddarar Allah, tare da tabbatar musu cewa Hukumar za ta ci gaba da ba su shawarwari da jagoranci kan hanyoyin da suka dace.
Ya bayyana cewa masu niyyar zuwa Hajjin da suke son mayar da kudin ajiyarsu zuwa Hajjin 2028, su yi hakan ta hannun Jami’in Rajistar Hajji na karamar hukumar da suka yi ajiyar kudin.
Haka kuma, wadanda suke son karbar kudin ajiyarsu, su bi wannan hanya ta hannun Jami’in Rajistar Hajji na karamar hukumar da suka yi ajiyar kudin tun farko.
Sakataren Dindindin ya tabbatar wa masu niyyar zuwa Hajji cewa Hukumar za ta ci gaba da tabbatar da gaskiya, adalci da rikon amana a dukkan harkokin rijistar Hajji, tare da gudanar da ayyukanta bisa ka’idoji da adadin kujerun da hukumomin da abin ya shafa suka ware.
Ya kuma bukaci Mataimakan Jami’an Rajistar Hajji da su ci gaba da wayar da kan masu niyyar zuwa Hajji kan muhimmancin bin matakan aikin Hajji, ka’idoji da kuma wa’adin da hukumomin da abin ya shafa suka kayyade.
Taron ya samu halartar jami’an gudanarwa na Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Sokoto da kuma Mataimakan Jami’an Rajistar Hajji guda 23 daga kananan hukumomin jihar.

