A wani babban mataki na inganta shirye-shiryen aikin hajjin bana, hukumar jin dadin alhazai ta jihar Kano ta kaddamar da wani kwakkwarar tawagar tallafawa alhazai mai dauke da mutane 300 domin biyan bukatun alhazan da za su tafi kasar Saudiyya.
Karanta labari makamancin wannan : 2025 Hajj: Hukumar Alhazai ta Kano ta sanar da ranar da Alhazai Zasu Fara Tashi
A yayin taron wayar da kan masu ruwa da tsaki da aka gudanar a Kano, darakta Janar na hukumar Alhaji Lamin Rabi’u Danbappa ya bayyana cewa an raba tawagar zuwa kwamitoci na musamman guda bakwai. Kowace tawaga in ji shi, an tsara ta ne don gudanar da wani muhimmin al’amari na aikin hajji, tun daga jagorar ibada zuwa kiwon lafiya da yada labarai.
“Wadannan kwamitocin ba sunaye ne kawai a kan takarda ba,” in ji Danbappa. “Su ne makamanmu na aiki don tabbatar da cewa kowane mahajjaci na Kano yana cikin koshin lafiya, sannan kuma yana da karsashi a duk lokacin aikin Hajji.”
Kwamitin bitar alhazai karkashin jagorancin Sheikh Tijjani Sani Mai Hula, ya kuduri aniyar daukar alhazai ta hanyar horo mai inganci da kuma shirin bada mai inganci
Dangane da ladabtarwa na cikin gida da warware rikici, Barista Ibrahim Haruna Khalil shi ne jagoran kwamitin kotun. Haka kuma a sahun gaba akwai kwamitin Hisbah karkashin jagorancin Dr. Mujahiddeen Aminuddeen, wanda aka dorawa alhakin inganta dabi’ar Mahajjata.
Sai kuma Dokta Ibrahim Musa da tawagarsa ne za su kula da ayyukan jinya, yayin da Sanusi Kabir da kwamitin kula da muhalli za su kula da matsalolin muhalli – musamman tsaftar gidaje.
Domin sanar da jama’a halin da ake ciki, Ibrahim Adam shi zai jagoranci ayyukan kwamitin yada labarai, yayin da Ishaq Abdullahi zai lura fannin sadarwa na zamani ta hanyar kwamitin Social Media.
Alhaji Danbappa ya yabawa Gwamna Abba Kabir Yusuf bisa irin goyon bayan da yake ba shi, inda ya ce an samar da dukkan kayan aiki da ake bukata domin gudanar da ayyuka cikin sauki.
Ya kara da cewa “Gwamna ya bamu duk abin da muke bukata, yanzu ya rage mana mu yiwa Kano alfahari.”
Taron ya hada wakilai daga masallatai, cibiyoyin kiwon lafiya,maniyyata aikin Hajji, da kungiyoyin farar hula, duk sun yi alkawarin bayar da goyon bayansu don tabbatar da samun kwarewa mai kyau da ruhi ga maniyyatan Kano.