Hukumar Royal Commission for Makkah City and the Holy Sites ta kammala dukkan shirye-shiryen da suka shafi wuraren Miqat domin tunkarar Hajjin shekarar 1447 Hijira, a wani mataki na inganta ayyuka da sauƙaƙa zirga-zirgar alhazai.
Shugaban Hukumar (CEO), Injiniya Saleh bin Ibrahim Al-Rasheed, ya bayyana cewa yanzu wuraren sallah a Miqat sun samu ƙarin faɗi, inda za su iya ɗaukar sama da maza 6,600 da kuma kusan mata 3,200. Haka kuma, an samar da dubban wuraren ajiye motoci da ɗaruruwan bandakuna masu inganci domin biyan bukatun alhazai.
Inganta Kayayyakin More Rayuwa
An gudanar da manyan gyare-gyare a wasu muhimman wuraren Miqat.
A Wadi Mahram, an gyara tsarin ruwan sha gaba ɗaya domin tabbatar da wadatar ruwa. A Al-Sayl Al-Kabir kuwa, an samar da tsarin dumama ruwa (central heating) da ke kula da bandakuna sama da 900, don ƙara jin daɗin masu ibada.
A ɓangaren tsaro, an girke sama da kyamarori 230 na sa ido a wuraren Miqat da kuma a masallatai da ke kewaye da Kaaba, domin ƙarfafa tsaro da kulawa yayin aikin Hajji.
Sauƙaƙa Hanya da Ayyuka
An kuma samar da sabbin alamun hanya (signage) domin jagorantar alhazai da nuna musu hanyoyin da za su bi cikin sauƙi. Haka zalika, an miƙa wuraren aiki ga ƙungiyoyin da ke gudanar da ayyuka, yayin da aka kafa rumfunan hidima na wucin gadi a wurare daban-daban don taimaka wa alhazai.
Wannan mataki na nuna ƙoƙarin Saudiyya na ci gaba da tabbatar da gudanar da Hajji cikin tsari, sauƙi da kwanciyar hankali ga al’ummar Musulmi daga sassa daban-daban na duniya.

