Taron gabatar da rahoton ya samu halartar Amirul Hajjin Jihar Jigawa, Mai Martaba Sarkin Dutse, Alhaji Hamim Muhammad Nuhu Sanusi.
A sanarwar da a hulda da jama’a na Hukumar, Habibu Yusuf Babura ya sanyawa hannu, yace a yayin gabatar da rahoton, Darakta-Janar na Hukumar, Alhaji Ahmad Umar Labbo FCFA, ya bayyana nasarorin da hukumar ta samu, waɗanda suka sanya Jihar Jigawa ta zama ta farko a cikin hukumomin jin daɗin mahajjata a faɗin ƙasar nan, bayan da a baya take matsayi na 24. Ya ce nasarar ta samu ne sakamakon jajircewar hukumar wajen gudanar da ayyukanta cikin gaskiya da adalci.
A matsayin wata alama ta nuna gaskiya da riƙon amana, hukumar ta mayar da sama da Naira miliyan 27 zuwa baitulmalin jihar, tare da mayar wa mahajjata sama da Naira miliyan 43 da suka rage daga kuɗaɗen Hadaya.
Darakta-Janar ɗin ya bayyana godiyarsa ga Gwamna Namadi bisa irin ci gaba da goyon baya da haɗin gwiwar da yake bai wa hukumar, wanda ya ce ya taimaka matuka wajen samun nasarorin da hukumar ke samu a kai a kai.
Ya kuma nuna godiya bisa amincewa da sakin sama da Naira biliyan 3.5 domin biyan kuɗaɗen ajiyar kujerun Hajji.
A nasa ɓangaren, Gwamna Namadi ya yabawa Darakta-Janar, Alhaji Ahmad Umar Labbo FCFA, a matsayin ƙwararren ma’aikacin gwamnati mai matuƙar sadaukar da kai. Ya bayyana cewa gaskiyarsa da rashin karkata sun taimaka wajen ɗaga martabar jihar zuwa wani matsayi na musamman, inda ya ƙarfafa shi da ya ci gaba da tafiya a kan tafarkin gaskiya da adalci.
Gwamnan ya kuma yaba da irin jagorancin da Amirul Hajji ya nuna wajen gudanar da aikin Hajjin jihar.
A jawabinsa, Amirul Hajj ya bayyana cewa sama da shekaru 35 na ƙwarewar Darakta-Janar ɗin a fannin sun taka muhimmiyar rawa wajen samun waɗannan nasarori, ciki har da ɗaukakar da jihar ta samu a matsayin ta farko a jerin hukumomin jin daɗin mahajjata na ƙasa, da kuma samar da wasu ayyuka kamar kula da lafiyar idon mahajjatan Jigawa kyauta.

