Babban Sakataren Hukumar Jin Daɗin Alhazan Jihar Sakkwato, Alhaji Ibrahim Umar JJ, ya halarci wani muhimmin taro da Hukumar Alhazai ta Ƙasa (NAHCON) ta shirya tare da Hukumomin Jin Daɗin Alhazai na Jihohi, a wani ɓangare na shirye-shiryen gudanar da aikin Hajjin shekarar 2027.
A sanarwar da Shugaban sashen yada labarai da sadarwa na Hukumar, Faruku Umar ya fiyar, yace Shugaban Hukumar NAHCON kuma Babban Jami’in Gudanarwarta, Mai Girma Ambasada Ismail Abba Yusuf, ne ya jagoranci taron, inda ya gabatar da jawabin buɗe taro tare da bayyana tsare-tsaren hukumar na tabbatar da nasarar gudanar da aikin Hajjin 2027.
Babban Sakataren ya samu rakiyar Daraktan Gudanarwa na Hukumar, Alhaji Ladan Ibrahim.
Muhimman batutuwan da aka tattauna sun haɗa da sabon tsarin rabon kujerun alhazai ga jihohi domin Hajjin 2027, yadda za a yi amfani da kujerun da aka ware, da kuma wa’adin kammala rajistar maniyyata. Haka kuma, an saurari martanin Shugaban Ƙungiyar Shugabannin Hukumomin Jin Daɗin Alhazai na Jihohi, tare da tattauna wasu batutuwan da suka shafi shirye-shiryen aikin Hajji.
Taron na daga cikin matakan farko da NAHCON ke ɗauka domin tabbatar da ingantaccen tsari da haɗin kai wajen gudanar da aikin Hajjin 2027. Haka kuma, ya bai wa masu ruwa da tsaki damar musayar ra’ayoyi da ƙarfafa haɗin gwiwa wajen inganta gudanar da harkokin Hajji a faɗin ƙasar nan.
Halartar tawagar Jihar Sakkwato a taron na nuna ƙudirin Hukumar Jin Daɗin Alhazan Jihar na ci gaba da aiwatar da manufofin NAHCON, tare da tabbatar da samar wa maniyyatan jihar ingantaccen shiri a dukkan matakan shirye-shiryen Hajjin 2027.

