Kasar Saudiyya ta kaddamar da sabon tsarin sabunta izinin zama (Iqama) mai sassauci ga ma’aikatan gida, wanda zai bai wa masu daukar aiki damar sabunta izinin zama na gajerun lokuta daban-daban ta hanyar dandalin Absher.
KARANTA LABARI MAKAMANCIN WANNAN: Hajjin 2026: Saudiyya Ta Kaddamar da Horaswa Ga Malamai da Jagororin Maniyyata a Madina
Ma’aikatar Harkokin Cikin Gida ta Saudiyya, ta hannun Hukumar Fasfo ta Kasa (Jawazat), tare da hadin gwiwar Ma’aikatar Albarkatun Dan Adam da Ci gaban Jama’a da kuma dandalin Musaned, ne suka sanar da wannan sabon tsari.
A karkashin sabon tsarin, masu daukar aiki za su iya fitarwa ko sabunta iqama ga ma’aikatan gida da makamantansu na tsawon watanni 3, 6, 9, 12, 15, 18, 21 ko 24. A baya, ana takaita sabuntawar zuwa shekara daya ko biyu kacal.
Sabon tsarin ya kuma bai wa masu daukar aiki damar biyan kudin iqama gwargwadon lokacin da suka zaba. Ga izinin da aka fitar ko aka sabunta na watanni uku ko ninkin watanni uku, ana iya biyan kudin a kashi-kashi duk bayan watanni uku, maimakon biyan kudin gaba daya lokaci guda.
Ma’aikatar ta ce wannan sauyi zai taimaka wajen rage nauyin kudi a kan masu daukar aiki tare da ba su karin damar daidaita bukatun aikinsu.
Jami’an gwamnati sun bayyana cewa matakin na daga cikin kokarin Saudiyya na inganta ayyukan gwamnati ta hanyar fasahar zamani, fadada ayyukan dijital, saukaka hanyoyin gudanar da harkokin iqama, da samar da mafita masu inganci ga masu daukar aiki da ma’aikatan gida.

