Ma’aikatar Hajji da Umrah ta Saudiyya ta sanar da sabuwar doka da ta tanadi cewa duk wanda ya ziyarci Al-Rawdah Al-Sharifa a Masallacin Annabi da ke Madina, sai ya jira tsawon kwanaki 365 kafin ya sake samun sabon izinin ziyara.
Ma’aikatar ta ce ana samun izinin ziyartar Raudah ne ta manhajar Nusuk, inda kowane mutum zai iya samun izinin ziyara guda ɗaya a cikin kwanaki 365.
Bayan cikar wannan wa’adi na shekara guda, mai ziyara zai iya neman sabon izini, amma hakan zai kasance ne bisa cancantarsa da kuma samuwar guraben yin rajista.
Haka kuma, mutanen da suke kusa da Masallacin Annabi ﷺ a Madina za su iya amfani da sabis ɗin Instant Track domin neman izinin shiga Raudah, gwargwadon samuwar gurabe.
Ma’aikatar ta bayyana cewa wannan sabon tsarin na daga cikin matakan da ake ɗauka domin tsara yawan masu ziyara, sauƙaƙa zirga-zirga da kuma tabbatar da samun kyakkyawan yanayi ga masu ibada a Masallacin Annabi ﷺ.

