Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Sokoto (PWA) ta bayyana cewa tana samun gagarumin ci gaba wajen gudanar da aikin rajistar maniyyatan Hajjin 2027, musamman wajen ɗora bayanan E-Passport da kammala rajistar maniyyata a cikin tsarin kwamfuta.
A sanarwar da Shugaban sashen yada labarai da sadarwa na Hukumar, Faruku Umar ya fitar, hukumar ta ce ana gudanar da aikin ne bisa umarni da jadawalin da aka tsara domin shirye-shiryen Hajjin 2027, inda jami’an rajista ke ƙoƙarin tabbatar da cewa an shigar da bayanan dukkan maniyyatan da suka cika sharuddan rajista yadda ya kamata.
A cewar Hukumar, ci gaban da aka samu zuwa yanzu wani ɓangare ne na ƙudurin ta na tabbatar da cewa an gudanar da rajistar maniyyatan Hajjin daga Jihar Sokoto cikin tsari, gaskiya da inganci.
Saboda haka, Hukumar ta yi kira ga maniyyatan da ba su kammala abubuwan da ake buƙata domin rajista ba, musamman waɗanda ba su gabatar da fasfo na ƙasa da ƙasa (International Passport) mai inganci ba, da su gaggauta yin hakan domin kauce wa duk wata matsala da ka iya tasowa yayin da wa’adin rajista ke ƙaratowa.
Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Sokoto ta kuma yaba wa maniyyatan bisa haɗin kan da suke bayarwa, tare da tabbatar musu da cewa tana ɗaukar dukkan matakan da suka dace domin ganin an kammala aikin rajistar Hajjin 2027 cikin nasara.
Haka kuma, Hukumar ta ƙara jan hankalin maniyyata da su rika samun sahihan bayanai game da aikin Hajji daga Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Sokoto da sauran hanyoyin da aka amince da su, domin kauce wa yaɗuwar bayanan ƙarya da matsalolin da ba su da tushe.

