Ma’aikatar Harkokin Addini, Wa’azi da Shiryarwa ta ƙasar Saudiyya ta amince da buɗe wuraren sallar mata a dukkan masallatan da ke birnin Madina, domin gudanar da salloli biyar na farilla a kullum.
Ministan Harkokin Addini, Wa’azi da Shiryarwa na Saudiyya, Sheikh Dr. Abdullatif bin Abdulaziz Al-Sheikh, ne ya bayar da wannan amincewa.
A ƙarƙashin sabon umarnin, za a buɗe wuraren sallar mata a ƙananan masallatan unguwanni da kuma manyan masallatan Juma’a, wato Jawami, domin mata su samu damar gudanar da sallarsu a kan lokaci.
A baya, wasu daga cikin masallatan Madina kan buɗe wuraren sallar mata ne kawai a ranar Juma’a, lokacin watan Ramadan, sallar Idi ko kuma a wasu lokutan da ake samun cunkoso na masu ziyara.
Sabon matakin zai bai wa mata sauƙin samun wurin ibada a duk lokacin da suke cikin birnin Madina, musamman waɗanda ke aiki, siyayya, ziyara ko kuma tafiya.
Umarnin bai shafi Masallacin Annabi ﷺ, wato Masjid an-Nabawi, ba, domin tuni masallacin ke da manyan wuraren da aka ware domin sallar mata, waɗanda ake buɗewa akai-akai.
Reshen Ma’aikatar Harkokin Addini, Wa’azi da Shiryarwa na yankin Madina ne zai jagoranci aiwatar da wannan umarni, ƙarƙashin Darakta-Janar na reshen, Sheikh Osama bin Zaid Al-Madkhali.
Haka kuma, ma’aikatar ta tura jami’an mata domin taimakawa wajen kula da wuraren sallar mata da kuma tabbatar da tsaro, musamman a masallatan tarihi da ke Madina.
Jimillar mata 115 aka tura domin gudanar da aikin sa ido da tsaro a wuraren sallar mata na wasu daga cikin masallatan tarihi, ciki har da Masallacin Sayyid al-Shuhada, Qiblatain, Khandaq, Ghamama, Mustarah da Jumu’ah.
Ana sa ran wannan mataki zai ƙara sauƙaƙa wa mata mazauna Madina da kuma masu ziyartar birnin samun damar yin salla a cikin masallatai a lokutan salloli biyar na farilla.

