Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Kano ta umarci dukkanin mahajjatan da suka yi rajistar niyyar gudanar da aikin Hajjin 2027 da su gabatar da ingantattun fasfo ɗin tafiye-tafiye na ƙasa da ƙasa kafin ko a ranar 25 ga Agusta, 2026.
A cikin wata sanarwa da Jami’in Hulɗa da Jama’a na Hukumar, Sulaiman Abdullahi Dederi, ya sanya wa hannu, ya ce Darakta-Janar na Hukumar, Alhaji Abubakar Ibrahim Matawalle, ne ya bayar da umarnin, domin tabbatar da kammala rajista da tattara bayanan dukkanin mahajjatan cikin lokaci kafin fara shirye-shiryen aikin Hajjin.
Alhaji Abubakar Matawalle ya yi gargaɗin cewa duk wani mahajjaci da ya yi rajista amma bai gabatar da fasfo ɗinsa kafin ko a ranar da aka sanya ba, na iya rasa damar samun kujerar Hajji.
A cewar Darakta-Janar ɗin, an sanya wa’adin ne saboda buƙatar kammala shigar da bayanan mahajjata da sauran takardun da suka wajaba cikin lokacin da aka tsara, musamman ganin cewa ana sa ran za a rufe tsarin rajistar Hajjin na Saudiyya a ƙarshen watan Agusta.
Ya buƙaci dukkanin mahajjatan da ke Kano waɗanda ba su gabatar da fasfo ɗinsu ba da su gaggauta yin hakan, tare da tabbatar da cewa an miƙa takardun ga hukumomin da abin ya shafa kafin ko a ranar 25 ga Agusta, 2026.
Darakta-Janar ɗin ya jaddada cewa Hukumar ba za ta ɗauki alhakin duk wata matsala ko sakamakon da ka iya biyo bayan rashin bin wa’adin da aka sanya ba.
Don haka, Hukumar ta shawarci dukkanin mahajjatan da suka yi rajista da su ɗauki wannan umarni da matuƙar muhimmanci tare da tabbatar da bin ƙa’idodin da aka gindaya cikin wa’adin da aka kayyade.

