Hukumar Alhazai ta Ƙasa (NAHCON) da Ma’aikatar Harkokin Wajen Najeriya sun amince da ƙara ƙarfafa haɗin gwiwarsu domin inganta gudanar da aikin Hajji, ayyukan jakadanci da kula da jin daɗin alhazan Najeriya a Ƙasar Saudiyya.
An bayyana hakan ne lokacin da Shugaban Hukumar NAHCON kuma Babban Jami’inta, Ambasada Ismail Abba Yusuf, ya kai ziyarar girmamawa ga Ƙaramin Ministan Harkokin Waje, Ambasada Sola Enikanolaiye, a hedikwatar Ma’aikatar Harkokin Waje da ke Abuja.
A yayin ganawar, Ambasada Enikanolaiye ya sake jaddada kudirin Gwamnatin Tarayya na yin aiki kafada da kafada da NAHCON domin tabbatar da ingantaccen gudanar da aikin Hajji tare da samar da ingantattun ayyukan jakadanci da tallafi ga alhazan Najeriya da ke Saudiyya.
Tun da farko, Ambasada Ismail Abba Yusuf ya taya Ministan murnar nadin da aka yi masa, tare da jaddada muhimmancin diflomasiyya wajen tabbatar da nasarar gudanar da aikin Hajji.
Ya bayyana cewa, jigilar fiye da alhazan Najeriya 50,000 zuwa Saudiyya a kowace shekara na haifar da batutuwan jakadanci, diflomasiyya da walwalar alhazai, waɗanda ke buƙatar cikakken haɗin gwiwa tsakanin NAHCON, Ma’aikatar Harkokin Waje da kuma Ofisoshin Jakadancin Najeriya da ke Saudiyya.
Shugaban NAHCON ya kuma gabatarwa Ministan rahoton nasarar aikin Hajjin 2026, inda ya danganta wannan nasara da tsauraran matakan tantance masu ba da hidima, ingantaccen tsarin gudanar da kwangiloli da kuma ƙarfafa matakan tabbatar da gaskiya da riƙon amana.
Dangane da shirye-shiryen gaba, Ambasada Yusuf ya bayyana cewa an riga an fara shirye-shiryen aikin Hajjin 2027 bisa jadawalin da hukumomin Saudiyya suka gindaya. Ya kuma sanar da Ministan cewa an ware wa Najeriya kusan guraben aikin Hajji 50,000 na shekarar 2027.
Haka kuma, ya sanar da Ministan cewa hukumomin Saudiyya sun gabatar da shawarar mayar da tsarin gudanar da aikin Hajjin Najeriya zuwa tsarin da kamfanonin Jirgin Yawo masu zaman kansu za su fi taka rawa a cikinsa, lamarin da ake sa ran zai yi tasiri ga yadda za a gudanar da aikin Hajji a nan gaba.
(Hajj Panorama)

