Sabuwar Hanyar Third Ring Road Ta Rage Nisan Zuwa Masallacin Harami Da Kilomita 10
Tafiya zuwa Masallacin Harami a Makkah ta ƙara zama cikin sauƙi, bayan buɗe wani sabon ɓangare na hanyar Third Ring Road da ke cikin birnin.
Hukumar Royal Commission for Makkah City and Holy Sites ta bayyana cewa sabon ɓangaren hanyar ya rage nisan da ke tsakanin mahadar Prince Miteb da Masallacin Harami daga kilomita 16.5 zuwa kilomita 6.5, wato an rage kilomita 10 daga hanyar.
Hukumar ta ce wannan sabon ci gaba zai taimaka wajen inganta zirga-zirgar ababen hawa da rage cunkoso, musamman a lokutan cunkoson ababen hawa da kuma lokacin gudanar da ayyukan Hajji da Umrah.
Sabon ɓangaren hanyar mai tsawon kilomita 1.5 na daga cikin babban shirin kammala Third Ring Road, wadda tana ɗaya daga cikin manyan hanyoyin zobe guda huɗu da ke kewaye da birnin Makkah.
A cewar hukumar, sabuwar hanyar tana da ƙarfin ɗaukar ababen hawa har 170,000 a kowace rana, ta ɓangarorin biyu.
Hukumar ta ce aikin zai kuma taimaka wajen inganta tsaron ababen hawa tare da sauƙaƙa zirga-zirgar mazauna Makkah, mahajjata da sauran baƙi zuwa birnin.
Haka kuma, aikin ya rage nisan hanyar da ke tsakanin wannan yanki da Jamarat da ke Mina, daga kilomita 12 zuwa kilomita 4 kacal.
Buɗe hanyar na daga cikin manyan ayyukan da ake gudanarwa domin inganta hanyoyin sufuri a Makkah, rage cunkoso da sauƙaƙa zirga-zirgar alhazai da masu ziyartar wuraren ibada.

