Shugaban Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Sokoto, Alhaji Aliyu Musa, tare da Mai Ba Gwamna Shawara na Musamman, Alhaji Nasiru Ladan, sun yi addu’o’i na musamman domin samun ci gaba da dorewar zaman lafiya, haɗin kai da ci gaban Jihar Sokoto.
A cewar Shugaban sashen yada labarai da sadarwa na Hukumar Faruku Umar, yace an gudanar da wadannan addu’o’i ne a cikin masallacin Manzon Allah (SAW) mai albarka da ke Madina, wato Masallacin Annabi (Al-Masjid an-Nabawi), inda a halin yanzu suke kasar Saudiyya.
A yayin addu’ar, sun roƙi Allah Madaukakin Sarki da Ya ba Gwamnan Jihar Sokoto, Alhaji Dr. Ahmad Aliyu Sokoto, kariya da hikima yayin da yake ci gaba da jagorantar jihar zuwa ga cigaba mai ɗorewa da wadata.
Haka kuma sun yi addu’ar Allah Ya tabbatar da zaman lafiya, kwanciyar hankali da wadata ga al’ummar Jihar Sokoto, tare da saukar da albarkarsa ga shugabanni da dukkan al’ummar jihar.

