Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Jigawa ta sanar da kudin aikin Hajjin shekarar 2027, inda ta kayyade jimillar kudin Hajjin kan Naira miliyan 7,672,822 ga kowane mahajjaci.
A sanarwar da Jami’in hulda da jama’a na Hukumar, Habibu Yusuf Babura ya sanyawa hannu, tace Daraktan-Janar na Hukumar, Alhaji Ahmad Umar Labbo, FCFA, NFI, ya bayyana cewa mahajjatan da suka riga suka biya ajiyar farko ta Naira miliyan 7.5, za su biya karin Naira 172,822 domin kammala kudin Hajjin.
Alhaji Labbo ya ce wa’adin kammala dukkan biyan kudin Hajjin a jihar shi ne 18 ga Satumba, 2026.
Ya umurci jami’an shiyyoyi da su kara kokarin ganin dukkan mahajjatan da suka yi rajista sun kammala biyan kudaden da ake binsu cikin wa’adin da aka kayyade.
Daraktan-Janar din ya kuma bukaci jami’an da su kara kaimi wajen wayar da kan mahajjata da shirye-shiryen tafiya, duba da cewa an tsara fara jigilar mahajjatan jihar zuwa Saudiyya a ranar 26 ga Satumba, 2026.
Alhaji Labbo ya yabawa jami’an hukumar bisa hadin kai da goyon bayan da suke bayarwa, sannan ya nuna matukar godiyarsa ga Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, bisa goyon bayan da yake bai wa aikin Hajji, musamman samar da lamuni domin tabbatar da samun kujerun Hajji ga alhazai.

