Burin wasu ma’auratan ƙasar Turkiyya na sauke Farali ya cika bayan sun shafe shekaru 17 suna jiran samun damar zuwa aikin Hajji, sakamakon kuri’ar zaɓen mahajjatan shekarar 2027 da Hukumar Addini ta Turkiyya (Diyanet) ta gudanar.
An gudanar da kuri’ar ne a dakin taro na Şehit Ali Alıtkan da ke birnin Ankara, a gaban jami’in tabbatar da sahihancin takardu (Notary) da kuma ‘yan jarida, inda aka tantance sunayen mahajjatan da za su cike kujeru 84,942 da Saudiyya ta ware wa Turkiyya domin Hajjin 2027.
Daga cikin waɗanda suka yi nasara akwai Mehmet Bal da matarsa Birgül Bal, waɗanda aka zaɓa bayan sun shafe kusan shekaru biyu cif suna jiran wannan dama. Cikin tsananin farin ciki, Mehmet Bal ya kasa riƙe hawaye lokacin da aka sanar da sunansa.
Ya ce sun fara rajistar neman zuwa Hajji tun shekarar 2011, kuma yau Allah Ya amsa addu’arsu. Ya kuma bayyana fatan cewa ɗansa da matar ɗansa, waɗanda su ma suka yi rajista, za su samu wannan dama nan gaba.
Ita kuwa Birgül Bal ta bayyana wannan rana a matsayin mafi farin ciki a rayuwarta. Ta ce wannan ne karo na farko da aka gayyace su domin halartar wurin gudanar da kuri’ar, kuma nan take ta kira ‘ya’yansu ta hanyar kiran bidiyo domin sanar da su labarin, tare da yi musu addu’ar Allah Ya ba su damar gudanar da Hajji a nan gaba.
A bana, mutane 1,878,046 ne suka shiga kuri’ar, ciki har da 252,708 da suka yi rajista karo na farko, yayin da 1,625,338 suka sabunta rajistarsu bayan sun kasa samun dama a shekarun baya. Wannan ya nuna yadda ake da matuƙar buƙatar samun guraben aikin Hajji a Turkiyya.
Kuri’ar ta kuma haifar da lokuta masu cike da tausayawa da farin ciki.
Sevda Artuç ta samu labarin cewa ta yi nasara ne bayan kawarta Meryem Çınar ta duba sakamakon kuma ta kira ta domin taya ta murna.
Duk da cewa Meryem ta shafe shekaru tara tana jira ba tare da samun dama ba, ta nuna farin cikinta saboda nasarar kawarta tare da ci gaba da fatan ita ma za ta samu nata lokacin.
Haka kuma, wasu tsofaffin ma’aurata da suka shafe kusan shekaru 16 suna jira sun samu damar zuwa Hajjin bana. Sun ce a shekarun baya suna barin wannan dakin taro cikin baƙin ciki bayan rashin nasara, amma a wannan karon farin cikin da suka samu ya wuce misali, inda suka yi murnar tare da jikokinsu.
Shi ma Ekrem Can da matarsa sun samu damar zuwa Hajji bayan jiran shekaru 16. Ya ce wannan ne karo na farko da ya halarci wurin gudanar da kuri’ar, yayin da wani abokinsa da ya shafe shekaru 17 yana jira ya ci gaba da fatan samun nasara a shekaru masu zuwa.
Hukumar Diyanet ta bayyana cewa waɗanda suka yi nasara za su iya duba sakamakonsu ta shafin e-Devlet daga ƙarfe 8:00 na dare ranar 22 ga Yuli, sannan kuma za a aika musu da saƙon SMS domin tabbatar da nasararsu.
Za a gudanar da rajistar waɗanda aka zaɓa daga 30 ga Yuli zuwa 18 ga Agusta ta hanyar tsarin e-Devlet.
Ana sa ran jigilar mahajjatan Turkiyya zuwa ƙasar Saudiyya za ta gudana tsakanin 17 ga Afrilu zuwa 11 ga Mayu, 2027, yayin da za a dawo da su gida tsakanin 20 ga Mayu zuwa 15 ga Yuni, 2027.

