Darakta Janar na Hukumar Jin Daɗin Alhazan Jihar Kano, Alhaji Abubakar Ibrahim Matawalle, ya sake jaddada cewa ranar 25 ga Satumba, 2026 ita ce ranar ƙarshe ta biyan kuɗin ajiya da kuma yin rajistar Hajjin shekarar 2027.
A sanarwar da Jami’in hulda da jama’a na Hukumar Sulaiman Abdullahi Dederi ya fitar, Darakta Janar din ya bayyana cewa ba za a ba wa duk wani maniyyacin aikin Hajji gurbin zuwa Hajji ba bayan wa’adin.
Matawalle ya bayyana hakan ne yayin wani taro da Jami’an Alhazai na Ƙananan Hukumomi 44 na Jihar Kano, wanda aka gudanar a ɗakin taro na Hukumar.
Ya tunatar da cewa tun da farko Hukumar ta sanar da Naira miliyan 8 a matsayin kuɗin ajiyar Hajjin 2027, tare da ayyana ranar 25 ga Satumba, 2026 a matsayin ranar rufe rajista.
Darakta Janar din ya buƙaci dukkan maniyyata da su gaggauta kammala biyan kuɗin ajiyarsu da kuma yin rajista kafin wa’adin domin tabbatar da samun guraben Hajji.
Ya jaddada cewa ba za a ƙara wa’adin rajista ba, kuma ba za a ƙara ware wasu guraben Hajji ba bayan ranar rufewa.
Alhaji Matawalle ya sake tabbatar da kudirin Hukumar na gudanar da aikin Hajji cikin tsari, gaskiya da inganci.
Haka kuma ya ƙarfafa wa dukkan masu niyyar zuwa Hajji gwiwa da su cika dukkan sharuddan da ake buƙata kafin cikar wa’adin rajista.

