Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Kano ta rage adadin kuɗin farko da mahajjatan da ke shirin zuwa aikin Hajjin 2027 za su biya daga naira miliyan 8 zuwa naira miliyan 7.
Hukumar ta kuma tabbatar da cewa ranar 25 ga Agusta 2026 ita ce ranar ƙarshe da aka kayyade wa dukkan mahajjatan da suka yi rajista domin miƙa fasfo ɗinsu ga Hukumar.
Daraktan-Janar na Hukumar, Alhaji Abubakar Ibrahim Matawalle, ne ya bayyana hakan a wani taron manema labarai da ya gudanar a ofishinsa da ke Kano.
Matawalle ya ce matakin rage kuɗin ajiya da kuma sanya wa’adin miƙa fasfo na daga cikin matakan da Hukumar ke ɗauka domin tabbatar da kammala rajista, tattara bayanai da sauran shirye-shiryen Hajjin 2027 cikin lokacin da Hukumar Alhazai ta Najeriya (NAHCON) da hukumomin Saudiyya suka tsara.
Ya bayyana cewa duk wani mahajjaci da ya yi rajista amma bai miƙa fasfo ɗinsa ba, ya tabbatar da yin hakan kafin ko a ranar 25 ga Agusta 2026.
Daraktan-Janar ya ce wa’adin yana da muhimmanci domin bai wa Hukumar damar kammala dukkan takardun da suka dace da sauran shirye-shiryen Hajji kafin a rufe tsarin rajistar Hajji na Saudiyya, wanda ake sa ran zai kasance a ƙarshen watan Agusta.
Ya kuma gargadi mahajjatan da ba su miƙa fasfo ba cewa rashin yin hakan kafin wa’adin da aka sanya na iya jefa damar samun kujerar Hajji cikin haɗari.
Matawalle ya yi kira ga dukkan mahajjatan da abin ya shafa da su gaggauta miƙa fasfo ɗinsu, yana mai cewa Hukumar ba za ta ɗauki alhakin duk wata matsala ko sakamakon da zai biyo bayan rashin bin umarnin cikin lokacin da aka kayyade ba.
Ya buƙaci maniyyata, iyalansu da sauran masu ruwa da tsaki da su ɗauki wannan wa’adi da muhimmanci tare da tabbatar da cikakken bin umarnin.
Daraktan-Janar ya ce babban burin Hukumar shi ne tabbatar da cewa dukkan mahajjatan da suka cancanta kuma suka yi rajista an kammala musu takardu yadda ya kamata, tare da shirya su domin gudanar da aikin Hajji cikin sauƙi da nasara.
Matawalle ya tabbatar wa al’ummar Jihar Kano cewa Hukumar za ta ci gaba da gudanar da ayyukanta bisa ƙwazo domin tabbatar da gudanar da Hajjin 2027 cikin tsari da inganci.
Ya kuma yabawa Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, bisa irin goyon baya da kulawar da yake bai wa ayyukan Hukumar da jin daɗin alhazan Kano, a jihar da kuma a ƙasa mai tsarki.
(Pyramid FM)

