Hukumar Alhazai ta Najeriya (NAHCON) ta sanar da amincewa da kamfanonin jiragen sama guda biyar da za su gudanar da jigilar mahajjatan Najeriya zuwa aikin Hajjin shekarar 2027.
Hukumar ta ce amincewar ta biyo bayan cikakken bincike da tantancewa da Kwamitin Tantance Kamfanonin Jiragen Sama ya gudanar, inda aka mayar da hankali kan tsaron jiragen sama, karfin gudanar da aiki da kuma yanayin kudi na kamfanonin.
A sanarwar da Shugabancin Hukumar ya fitar, Kamfanonin jiragen saman da aka amince da su sun hada da:
Air Peace Limited
Flynas
Max Air Limited
Saudi Air
UMZA Aviation Services Limited
NAHCON ta bayyana cewa fara aikin kamfanonin zai kasance ne bayan sanya hannu kan yarjejeniyar jigilar alhazai da Hukumar, tare da cika dukkan sharuddan da Hukumar Kula da Sufurin Jiragen Sama ta Najeriya (NCAA) da kuma Hukumar Kula da Sufurin Jiragen Sama ta Saudiyya (GACA) suka gindaya.
Hukumar ta kara da cewa za a tsara adadin mahajjatan da kowanne kamfani zai dauka da kuma jadawalin tashin jirage tare da hukumomin jin dadin mahajjata na jihohi da kuma kamfanonin jiragen saman da aka amince da su.
NAHCON ta umurci kamfanonin da su bi dukkan ka’idojin aikin Hajjin 2027, ciki har da samar da tikitin jirgi da aka danganta da bayanan mahajjata da ke cikin tsarin Nusuk-Masar, da kuma tabbatar da bin dukkan ka’idojin tsaron jiragen sama.
Dangane da kayan tafiya, kowanne mahajjaci zai samu damar tafiya da akwatin kaya guda mai nauyin kilogram 32 da kuma karamin kaya na hannu mai nauyin kilogram 8, kamar yadda ka’idojin hukumomin da abin ya shafa suka tanada.
NAHCON ta yi kira ga dukkan masu ruwa da tsaki, musamman hukumomin jin dadin mahajjata na jihohi, mahajjata masu niyyar zuwa Hajji da kuma kamfanonin jiragen sama, da su ba da hadin kai domin tabbatar da gudanar da jigilar mahajjatan Najeriya cikin sauki, tsaro da kwanciyar hankali.

