Hukumar Alhazai ta Najeriya (NAHCON) ta sanar da kudaden da Gwamnatin Tarayya ta amince da su domin gudanar da aikin Hajjin 2027.
A sanarwar da Shugabancin Hukumar ta sanyawa hannu, Hukumar ta ce an tsara kudaden ne bayan tattaunawa da shugabannin Ƙungiyar Hukumomin Jin Dadin Alhazai na Jihohi, da masu samar da ayyuka a Masarautar Saudiyya, tare da la’akari da farashin canjin kuɗi da kuma tsadar ayyukan da ake bayarwa.
Kudaden Hajjin da aka amince da su sun bambanta bisa ga yankin da mahajjata za su tashi, kamar haka:
– Yankin Maiduguri/Yola: N7,560,822.00
– Yankin Arewa: N7,672,822.00
– Yankin Kudu: N7,882,822.00
NAHCON ta ce mahajjatan da suka riga suka biya Naira miliyan 5 za su biya sauran kuɗin da ya rage domin kammala rajistarsu.
Sabbin masu niyyar zuwa Hajji kuma an shawarce su da su biya kuɗin ta hannun Hukumomin Jin Dadin Alhazai na Jihohinsu, ko kuma ta bankunan da ke cikin tsarin Hajj Savings Scheme (HSS) da aka amince da su.
Hukumar ta kuma sanya 26 ga Satumba 2026 a matsayin ranar ƙarshe kuma ta ƙarshe da za a kammala ɗora bayanan biometric na masu niyyar zuwa Hajji a dandalin dijital na Nusuk-Masar, bisa tsarin da Ma’aikatar Hajji da Umrah ta Saudiyya ta gindaya.
Haka kuma, NAHCON ta umurci jihohi da su kammala tura dukkan kuɗaɗen Hajjin 2027 zuwa Hukumar nan da 2 ga Disamba 2026.
NAHCON ta jaddada cewa ba za a ƙara wa’adin da aka sanya ba, saboda daidaita bayanan mahajjata da kuma rabon kujerun Hajji sun dogara ne da cikar biyan kuɗaɗen cikin lokaci.
Hukumar ta kuma yi gargaɗin cewa rashin cika waɗannan wa’adi na iya haifar da soke ko rasa kujerun Hajjin da aka ware wa mahajjata.

