Daga Aliyu Zakari Bauchi Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Bauchi ta sanar da fara karɓar kuɗin kujerun aikin Hajjin shekarar 2027, tare da yin kira ga duk masu niyyar zuwa aikin Hajji daga sassan jihar da su yi amfani da wannan damar ta biyan kuɗi da wuri domin kauce wa matsalolin da kan taso a lokacin ƙarshe.
Sakataren Zartarwa na Hukumar, Imam Abdulrahman Ibrahim Idris, ne ya bayyana hakan yayin da yake zantawa da manema labarai a ofishinsa dake Bauchi.
Ya ce sayar da kujerun Hajji da karɓar kuɗin kujeru za su fara ne daga ranar Litinin, 6 ga Yulin 2026, kuma za su ci gaba har zuwa ranar 25 ga Satumban 2026. Ya jaddada cewa masu niyyar aikin Hajji su tabbatar sun kammala biyan kuɗinsu cikin wa’adin da aka sanya.
Imam Abdulrahman ya bayyana cewa wannan tsarin fara karɓar kuɗi da wuri ya yi daidai da jadawalin shirye-shiryen aikin Hajji na Masarautar Saudiyya, wanda ke buƙatar ƙasashen da ke halartar aikin Hajji su kammala shirye-shiryensu tun kafin lokacin tafiya.
Ya ƙara da cewa hukumomin Saudiyya za su dakatar da bayar da bizar Hajji daga ranar 28 ga Janairun 2027, yayin da ake sa ran fara jigilar maniyyatan Najeriya zuwa ƙasa mai tsarki daga ranar 8 ga Afrilun 2027.
Sakataren Zartarwan ya yi kira ga duk masu niyyar aikin Hajji a jihar da su biya kuɗinsu kai tsaye ta Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Bauchi ko kuma ta hannun Jami’an Harkokin Hajji na ƙananan hukumominsu.
Ya tabbatar da cewa hukumar na ci gaba da jajircewa wajen tabbatar da gudanar da aikin Hajji cikin tsari, gaskiya da ingantaccen shiri domin amfanin dukkan alhazan jihar.

