Hukumar Alhazai ta Kasa (NAHCON) ta bukaci dukkan alhazan da suka gudanar da aikin Hajji da Umrah na shekarar 2026 da su gabatar da korafe-korafensu, ra’ayoyinsu da shawarwarinsu kan ayyukan da mutane ko hukumomin da suka gudanar da hidimomin Hajji da Umrah suka yi musu.
Hukumar ta bayyana cewa wannan na daga cikin bitar da take yi bayan kammala aikin Hajjin 2026 domin tantance yadda aka gudanar da ayyukan tare da inganta hidimomin Hajji da Umrah a nan gaba.
A cewar NAHCON, bayanan da alhazai za su gabatar za su taimaka wajen gano wuraren da ake bukatar gyara, tare da zama muhimmin abin dubawa wajen sabunta lasisin masu ba da hidima, ciki har da kamfanonin yawon Hajji da Umrah, Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihohi, kamfanonin jiragen sama, kamfanonin dakon kaya, masu samar da abinci, masu masauki da sauran masu ruwa da tsaki.
Hukumar ta kuma bukaci sauran masu ruwa da tsaki da jama’a su gabatar da shawarwari masu amfani da za su taimaka wajen kara inganta yadda ake gudanar da harkokin Hajji da Umrah a Najeriya.
NAHCON ta bukaci duk wanda zai gabatar da korafi, ra’ayi ko shawara ya sanya cikakken adireshinsa, sannan ya aika da takardar zuwa:
Shugaban Hukumar/ Babban Jami’in Gudanarwa (Chairman/CEO)
National Hajj Commission of Nigeria (NAHCON)
Plot 991/992 Zakariya Maimalari Street
Central Business District, Abuja
P.M.B. 375, Abuja.
Haka kuma ana iya aika da korafe-korafen ko shawarwarin ta hanyar imel zuwa info@nigeriahajjcom.gov.ng, nahconoperations@gmail.com, ko nahcon2006info@gmail.com kafin ko a ranar 31 ga Yulin 2026.
Domin neman karin bayani ko taimako, hukumar ta bukaci a tuntubi Sashen Ayyukan Hajjli (Operations Department) ta lambobin waya 07039059256 ko 08074160299, ko kuma ta lambar WhatsApp ta hukuma +234 907 180 0007.
NAHCON ta jaddada cewa wannan mataki na daga cikin nauyin da doka ta dora mata na sa ido, tsarawa da inganta ayyukan dukkan hukumomi da kungiyoyin da ke da alhakin shirya da gudanar da harkokin Hajji da Umrah a Najeriya.

