Shugaban Hukumar Alhazai ta Kasa, wato National Hajj Commission of Nigeria (NAHCON), Ambasada Ismail Yusuf Abba, ya sake jaddada kudirin hukumar na kara inganta ilimantar da alhazai da kuma shirya su ta fuskar addini gabanin aikin Hajjin shekarar 2026.
KARANTA LABARI MAKAMANCIN WANNAN : Malaman Addini na Kogi Sun Yabawa Shugaban NAHCON, Sun Bukaci Gyara A Wasu Sassa
Shugaban ya bayyana hakan ne yayin wata ganawa ta musamman da kuma kaddamar da Tawagar Malaman Bitar alhazai ta shekarar 2026, wanda aka gudanar ranar Laraba, 22 ga Afrilu, 2026, a dakin taro na Hajj House da ke Abuja.
A cewar Mataimakiyar Darakta ta Sashen Yada Labarai da Wallafe-wallafe, Fatima Sanda Usara, taron ya hada manyan malamai 120 daga sassa daban-daban na kasar nan. Daga cikinsu akwai Farfesa Mansur Ibrahim Sokoto, Sheikh Bala Lau, Sheikh Abdulmuhyi Nasir mai wakiltar Sheikh Sani Yahaya Jingir, Sheikh Abdulrahman Olanrewaju Ahmed, Sheikh Nasir Adam, Sheikh Muhammad Kabir Haruna Gombe, Sheikh Usman Usman Dahiru Bauchi, da kuma Dr Isa Akindele Solahuddeen, tare da sauran su.
Babban abin da aka fi mayar da hankali a kai shi ne ilimantar da alhazai da kuma shirya su yadda ya kamata. Shugaban ya bukaci malaman da su taimaka wa hukumar wajen gudanar da tarukan wayar da kai cikin harsuna daban-daban kafin da lokacin aikin Hajji. Ya jaddada cewa ya kamata su mayar da hankali wajen koya wa alhazai muhimman ka’idoji da rukunnan Hajji domin su iya gudanar da ibadarsu yadda ya dace.
Haka kuma, ya nanata muhimmancin ci gaba da ba alhazai jagoranci tare da amsa tambayoyinsu cikin gaggawa, musamman a lokutan da ka iya shafar ingancin aikin Hajjin su.
Tawagar malaman za ta kuma shirya zaman addu’o’i na musamman a wurare masu muhimmanci yayin aikin Hajji, musamman a Arafat, domin yi wa Najeriya addu’ar zaman lafiya, tsaro, hadin kai da ci gaban tattalin arziki.
Farfesa Bashir Umar ya bukaci dukkan malaman da su jagoranci al’ummominsu wajen yin addu’ar samun zaman lafiya a zabukan kasar nan, ganin cewa aikin Hajjin na 2026 zai zo ne a daidai lokacin shirye-shiryen zaben 2027.
A nasu bangaren, malaman sun jaddada muhimmancin shirya zukatan alhazai, tare da karfafa hadin kai, ikhlasi, hakuri da kuma cikakken mika wuya ga Allah, yayin da suka sake bayyana cewa aikin Hajji wata ibada ce mai sauya rayuwa. Tawagar ta kuma tabbatar da shirinta na tabbatar da alhazan Najeriya sun samu cikakkiyar kwarewa ta ruhaniya.

