Hukumar Jin Daɗin Alhazan Jihar Kaduna tana sanar da daukacin al’umma cewa an fara rajistar aikin Hajjin shekarar 2027.
A cewar Jami’in Hulda da Jama’a na Hukumar Ibrahim Datti, ana buƙatar duk masu niyyar zuwa aikin Hajji su ziyarci ɗaya daga cikin ofisoshin Alhazai na ƙananan hukumomi 23 da ke faɗin jihar ko kuma Hedikwatar Hukumar da ke kan Titin Katsina a Kaduna domin karɓar takardar biyan kuɗi (bank payment teller) ta hukuma tare da fara rajista.
Hukumar tana jaddada cewa duk kuɗaɗen Hajji dole ne a biya su ne kawai cikin asusun bankin hukuma na Hukumar Jin Daɗin Alhazan Jihar Kaduna. Hukumar ba ta karɓar kuɗi a hannu, kuma ba ta amince da biyan kuɗi cikin asusun wani mutum ba.
Saboda haka, ba za ta ɗauki alhakin duk wata asara da ta taso sakamakon biyan kuɗi ta hanyar da ba ta hukuma ba.
Duk da cewa Hukumar Alhazai ta Ƙasa (NAHCON) ta amince da mafi ƙarancin kuɗin ajiya na farko na Naira miliyan 4 (₦4,000,000), Hukumar Jin Daɗin Alhazan Jihar Kaduna tana ƙarfafa masu niyyar zuwa Hajji da su ajiye Naira miliyan 8 (₦8,000,000) yayin da ake jiran sanar da cikakken kuɗin Hajjin 2027.
Hukumar ta kuma yi kira ga masu niyyar zuwa Hajji da su kammala rajistarsu da wuri.
Ta tunatar da cewa a Hajjin da ya gabata, wasu sun rasa damar zuwa Hajji saboda rashin kammala rajistarsu kafin wa’adin da aka ƙayyade. Don kauce wa maimaita hakan, ana shawartar kowa da ya yi rajista cikin gaggawa.
Hukumar ta bayyana cewa 26 ga Satumba, 2026 ita ce ranar ƙarshe ta rajistar Hajjin 2027 kamar yadda NAHCON ta ayyana, kuma ba za a karɓi wata rajista bayan wannan rana ba.
Domin samun ƙarin bayani, a ziyarci Hedikwatar Hukumar Jin Daɗin Alhazan Jihar Kaduna da ke kan Titin Katsina a Kaduna ko kuma ɗaya daga cikin ofisoshin Alhazai na ƙananan hukumomi 23, ko a kira lambar waya: 0701 070 1561.

