Hukumar Alhazai ta Kasa (NAHCON) ta bayyana cewa bidiyon da ke yawo a kafafen sada zumunta wanda ke ikirarin cewa an bar wasu alhazan Jihar Adamawa ba tare da masauki ba har tsawon kwanaki biyu a Makkah, ba gaskiya ba ne.
Bayan samun rahoton, NAHCON ta tura tawagar bincike zuwa wurin da aka dauki bidiyon. Sakamakon binciken ya nuna cewa, sabanin yadda aka yada rahoton, alhazan sun isa Makkah ne a daren ranar 13 ga Mayu. Yayin da wasu ke jiran a tantance musu dakunansu, wasu kuma sun tafi Harami domin gudanar da Umrah.
Wannan ne ya haifar da rashin fahimta yayin rabon dakuna, domin wasu daga cikin wadanda aka gani a bidiyon an riga an ware musu dakuna amma ba su san inda suke ba.
Da dawowarsu, jami’ai sun kula da su tare da kammala tsarin ba su masauki.
An dauki bidiyon ne a lokacin da ake ci gaba da aikin rabon dakuna, lamarin da ya haifar da mummunar fahimta ga jama’a. NAHCON ta tabbatar da cewa an riga an samar wa dukkan alhazan da abin ya shafa masauki yadda ya kamata.
Hukumar tana kira ga alhazai da jami’ai da duk wanda ya fuskanci wata matsala da ya fara tantance gaskiyar lamarin tare da tuntubar jami’an Hukumar Jin Dadin Alhazai ta jiharsa ko kuma NAHCON kafin yada bayanan da ka iya yaudarar jama’a.
NAHCON tare da Hukumomin Jin Dadin Alhazai na Jihohi na ci gaba da jajircewa wajen tabbatar da jin dadi da walwalar dukkan alhazan Najeriya.

