’Yan Najeriya sun bukaci Babban Bankin Najeriya (CBN) da ya dage shirin bayar da Basic Travel Allowance (BTA) ga mahajjatan Najeriya ta hanyar katin ATM, bisa damuwar da ake da ita kan yiwuwar katunan kin aiki da kuma matsalolin da mahajjata za su iya fuskanta wajen samun kudinsu a Saudiyya.
Ana sa ran fara aiwatar da wannan tsarin a bana, wanda zai kawo gagarumin sauyi daga tsarin da aka saba amfani da shi na bai wa mahajjata BTA a matsayin tsabar kudi.
Sai dai sakamakon wani bincike da kafar Hajj Reporters ta gudanar ta yanar gizo ya nuna ra’ayoyi mabanbanta, inda mafi yawan wadanda suka amsa tambayoyin suka nuna goyon baya ga ci gaba da amfani da tsarin tsabar kudi. Wasu kuwa sun goyi bayan tsarin katin, suna masu cewa ya kamata Najeriya ta rungumi tsarin biyan kudi na zamani.
Daya daga cikin wadanda suka amsa tambayoyin, Abdulwahab Hafis, ya goyi bayan shirin, yana mai cewa zai rage matsin lambar da ke tattare da rike tsabar kudi da kuma rage hadarin mahajjata su rasa kudinsu.
Sai dai wani wakilin kamfanin tafiye-tafiye, Ibrahim Abubakar, ya nuna damuwa bisa abubuwan da suka faru a baya dangane da katunan BTA da aka bai wa wasu mahajjata.
A cewarsa, wasu mahajjatan da aka bai wa katunan BTA sun kasa amfani da su a Saudiyya saboda ba a kunna katunan ba. Ya ce kokarin warware matsalar ta hanyar kiran bankunan da suka bayar da katunan da kuma tura musu sakonnin imel bai yi nasara ba, domin a wasu lokuta ana umartar mahajjatan da abin ya shafa su koma Najeriya domin ziyartar reshen banki.
Abubuwan da suka faru, a cewar Abubakar, sun sanya wasu mahajjata suka kasance ba tare da damar samun kudinsu ba har sai da suka koma Najeriya, lamarin da ya karya manufar tsarin BTA. Ya kuma koka kan yadda wasu mahajjata ba su samu cikakken mayar da kudaden da aka cire musu a matsayin kudin gudanar da katunan ba.
Sai dai ya amince cewa tsarin bayar da BTA a matsayin tsabar kudi ma yana da nasa matsalolin. Ya yi zargin cewa wasu daga cikin wadanda suka amfana da kudaden BTA kan karkatar da dalolin zuwa kasuwar bayan fage maimakon amfani da su wajen biyan bukatunsu yayin aikin Hajji.
Shi ma wani mai suna Haruna Musa Gawain, ya yi gargadin cewa tsarin katin na iya haifar da manyan matsaloli, musamman ga mahajjatan karkara wadanda ba su da cikakkiyar masaniya kan yadda ake amfani da ATM.
Ya kuma yi nuni da karancin ATM a wasu wuraren da ake saukar da mahajjatan Najeriya, ciki har da Misfalah da Shara Mansur a Makkah.
Gawain ya ba da shawarar cewa idan aka fara amfani da tsarin katin, hukumomin jin dadin mahajjata na jihohi su samar da karin tallafi da jagoranci ga mahajjata wajen cire kudinsu da gudanar da hada-hadar kudi a Saudiyya.
Haka kuma, Taiye Iliyasu ya nuna shakku kan ko akwai isassun na’urorin ATM a kewayen Masallacin Harami, Madina da otal-otal din da mahajjata ke sauka, tare da tambayar ko akwai isassun na’urorin POS a wajen ’yan kasuwar yankunan.
Ya ba da shawarar cewa amfani da katin ATM ya kasance zabi ga mahajjata, maimakon a mayar da shi dole.
Sai dai wasu daga cikin wadanda suka amsa binciken sun goyi bayan tsarin biyan kudi na zamani.
Mustapha Tafarki ya ce mahajjata, ciki har da wadanda suka fito daga karkara, za su iya saba da amfani da tsarin hada-hadar kudi ta zamani a hankali. Shi kuwa Babagana Musa ya ce tsarin zai taimaka wajen sanya Najeriya cikin sahun kasashen da ke bin sabbin fasahohin zamani.
Dayab Babangida ya ba da shawarar cewa a sanya koyar da yadda ake amfani da katin ATM cikin shirye-shiryen wayar da kan mahajjata da hukumomin jin dadin mahajjata na jihohi ke gudanarwa kafin tafiya.
Shi ma Odebunmi Eta Oko ya bayyana tsarin a matsayin kyakkyawan ci gaba, yana mai cewa ’yan kasuwa da dama a Saudiyya suna karbar biyan kudi ta katin.
Sai dai Suleiman Suleiman ya ce irin wannan shawara ta taba tasowa a shekarun baya, amma ba a aiwatar da ita ba saboda damuwar da hukumomin jin dadin mahajjata na jihohi suka nuna da kuma irin yanayin da mahajjatan Najeriya suke ciki.
Dangane da damuwar da aka bayyana kan gazawar katunan a kasashen waje a baya, da kuma samuwar ATM da POS a wuraren da mahajjata ke zama, wadanda suka bayyana ra’ayoyinsu sun bukaci CBN da hukumomin Hajji da abin ya shafa da su kara yin tuntuba da masu ruwa da tsaki, tare da samar da ingantattun matakan kariya kafin fara aiwatar da sabon tsarin.
( Independent Hajj Reporters)

