Alhazan Jihar Kano na ci gaba da samun walwala a Mina, inda aka samar musu da wadataccen abinci da kulawar lafiya yayin da aka fara gudanar da ayyukan Hajjin shekarar 2026 a ranar Litinin.
Jimillar alhazai 3,620 daga Jihar Kano na daga cikin miliyoyin Musulmai da ke gudanar da aikin Hajjin bana.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwar manema labarai da shugaban tawagar yada labarai ta ayyukan Hajjin Kano 2026, Mustapha Muhammad, ya fitar.
Da dama daga cikin alhazan Kano sun bayyana gamsuwarsu kan ire-iren abincin da ake basu tun bayan isowarsu Mina, tare da irin kulawar lafiya da ake samar musu.
Ziyarar da aka kai dakin girki inda ake hada abinci ta nuna masu dafa abinci suna ta shirya abincin rana wanda ya kunshi shinkafa, kaza, lemo, ruwa da lemu.
Haka kuma, ana samar da shayi da kofi a wurare daban-daban tun daga safe har zuwa yamma, yayin da aka tanadi firij-firij cike da ruwa da nau’o’in lemo daban-daban da alhazai ke samu kyauta a kowane lokaci.
Hakazalika, ziyarar da aka kai asibitocin da Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Kano ta kafa a Mina ta nuna jami’an lafiya suna kula da alhazan da ke bukatar kulawar lafiya.
A gefe guda kuma, Darakta Janar na Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Kano, Alhaji Abubakar Ibrahim Matawalle, an gan shi yana duba tantunan alhazai tare da tattaunawa da su domin gano duk wata matsala ko kalubale tare da magance su cikin gaggawa.
Wadannan matakai sun sanya alhazan Kano cikin walwala da annashuwa a tsawon zamansu a Mina.
“Ko akwai wata matsala?” wannan ita ce tambayar da Darakta Janar, Abubakar Ibrahim Matawalle, ya rika yi wa alhazai yayin da yake zagayawa tsakanin tantuna da wuraren ibada tare da yi musu addu’o’i.
Wannan na nuna irin kulawa da jajircewar Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Kano da kuma Gwamnatin Jihar Kano karkashin jagorancin Alhaji Abba Kabir Yusuf wajen tabbatar da jin dadin alhazan Kano.

