An gayyaci Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, domin halartar taron Future Investment Initiative (FII) karo na 10, wanda za a gudanar a birnin Riyadh na ƙasar Saudiyya a watan Oktoban wannan shekara.
Jakadan Masarautar Saudiyya a Najeriya, Yousef Mohammed Albalawi, ne ya miƙa wasiƙar gayyatar daga Mai Martaba Yarima Mohammed bin Salman bin Abdulaziz Al Saud, Yarima Mai Jiran Gado kuma Firaministan Masarautar Saudiyya, zuwa ga Mai Girma Shugaban Ƙasar Tarayyar Najeriya, Bola Ahmed Tinubu.
An miƙa wannan gayyata ne yayin wata ganawa da Shugaba Tinubu ya yi da Jakadan a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja a ranar Juma’a, 24 ga Yuli, 2026.
Shugaba Tinubu ya bayyana godiyarsa da matuƙar jin daɗinsa bisa wannan gayyata, tare da yaba kyakkyawar alaƙar da ke tsakanin Masarautar Saudiyya da Tarayyar Najeriya a fannoni daban-daban, yana mai jaddada muhimmancin ci gaba da ƙarfafa haɗin gwiwar ƙasashen biyu.
(IHR)

