An kaddamar da sabuwar cibiyar wayar da kai ta addini ta Tafi-Da-Gidanka a Masallacin Annabi (Masjid an-Nabawi) da ke Madina domin bai wa masu ibada da baƙi damar samun shiriya da amsoshin tambayoyinsu cikin sauƙi a ko’ina cikin harabar masallacin.
Shugaban Harkokin Addini na Masallacin Harami da Masallacin Annabi, Sheikh Dakta Abdulrahman bin Abdulaziz Al-Sudais, ne ya ƙaddamar da cibiyar a matsayin wani ɓangare na ƙoƙarin inganta ayyukan addini da kusantar da su ga masu ziyara.
Al-Sudais ya bayyana cewa an kafa cibiyar ne domin samar da saurin amsa tambayoyin baƙi da masu ibada, da kuma ƙara inganta ƙwarewarsu ta ibada da neman ilimin addini.
Ya ce hakan kuma zai ƙara tabbatar da matsayin Masallacin Annabi wajen yaɗa sahihan koyarwar Musulunci da kuma ƙarfafa manufar tsaka-tsaki (wasatiyya).
Cibiyar tana ba da ayyuka da suka haɗa da amsa tambayoyin addini kai tsaye, bayar da shawarwari bisa Shari’ar Musulunci, da kuma rarraba littattafai da kayayyakin wayar da kai.
Domin sauƙaƙa sadarwa da alhazai da baƙi daga ƙasashe daban-daban, cibiyar tana samar da waɗannan kayayyakin ilimantarwa cikin harsuna da dama, wanda zai taimaka wajen isar da saƙon addini ga miliyoyin masu ziyartar Masallacin Annabi.

