A cikin birnin Madinah, kusa da Masjid an-Nabawi, wasu iyalai daga ƙasar Pakistan (jihar Sindh) sun shafe kusan shekaru 70 suna hidimta wa baƙi da masu ziyara ta hanyar ba su shayi, kofi da abinci.
Wannan al’ada ta fara ne daga kaka (kakan iyalin), wanda ya kafa ƙaramin wajen sayar da abinci da ake kira “safra”. A yau, Mohammed Ali Abdul Rahman Al-Sindi ne ke jagorantar wannan hidima, kasancewarsa ɗan ƙarni na uku da aka haifa a Madinah.
Da farko an kafa wajen a yankin Al-Ainiyah, amma sakamakon faɗaɗa masallacin, mahaifinsa ya matsar da shi zuwa wani wuri. Daga bisani Mohammed ya karɓi ragamar aikin a shekarar 1428AH (kimanin 2007–2008), inda ya ci gaba da gudanar da hidimar da iyalinsu suka daɗe suna yi.
Duk da sauye-sauye da aka samu tsawon lokaci kamar canjin wurare da sauyin zamani manufar aikin ba ta canza ba: yi wa baƙin Manzon Allah (SAW) hidima da kyakkyawar niyya.
Baya ga hidimar yau da kullum, iyalan suna kuma shirya abincin buda baki (Iftar) kyauta akai-akai. Suna yin hakan a ranakun Litinin da Alhamis, da kuma ranakun farin wata (13, 14 da 15 na kowane wata na Musulunci), da kuma duk tsawon watan Ramadan.
Iyalan sun samu cikakken gindin zama a Madinah, inda ‘ya’yan Mohammed suka yi karatu har suka kammala makarantar sakandare a garin. Wannan ya nuna yadda suka zama ɓangare na al’ummar garin.
Mohammed ya bayyana Madinah a matsayin ƙasa mai albarka da ta karɓi iyalinsa hannu bibbiyu tun tsawon shekaru. A cewarsa, wannan aiki ba kawai sana’a ba ce, illa wata babbar hidima ce ta addini da al’ada da yake fatan za ta ci gaba har zuwa gaba.

