Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Jigawa ta sanar da cewa dukkanin maniyyatan jihar za su rika samun abinci sau uku a kowace rana a lokacin gudanar da aikin Hajjin 2026.
KARANTA LABARI MAKAMANCIN WANNAN : Hukumar Alhazai Ta Jigawa Ta Ce Maniyata Fiye Da 1,000 Ne Suka Biya Kudin Kujerar Hajin Bana
A sanarwar da Jami’in hulda da jama’a na hukumar, Habibu Yusuf Babura ya fitar, ya ce Darakta Janar na Hukumar, Alhaji Ahmad Umar Labbo, ne ya bayyana hakan yayin da yake zantawa da manema labarai a ofishinsa. Ya ce an kirkiro wannan tsari ne domin inganta jin dadin alhazan Jigawa yayin zamansu a kasa mai tsarki.
A cewarsa, tsarin ciyarwar zai shafi dukkanin rukunin alhazai, har da masu bukatar abinci na musamman.
Babban Daraktan ya kara da cewa wannan shiri na samun cikakken tallafi ne daga Gwamnan Jihar Jigawa, Mai Girma Umar Namadi, wanda hakan ya sa Jigawa ta zama jiha daya tilo da ke samar da cikakken tsarin ciyarwa ga alhazanta.
Ya kuma bayyana godiya matuka ga Gwamna Namadi bisa irin goyon bayan da yake bai wa hukumar da kuma jajircewarsa wajen tabbatar da walwalar alhazai, yana mai cewa hakan na nuna kudirin gwamnati na samar da sauki da kwanciyar hankali ga alhazai yayin gudanar da aikin Hajji.

