Hukumar Alhazai ta kasa (NAHCON) ta gargadi al’umma game da wasu ‘yan damfara da hukumomin tafiye-tafiye marasa rajista da ke ikirarin suna iya samar da bizar Hajji duk da cewa an rufe bayar da bizar Hajjin 2026.
A cikin wata sanarwa da hukumar ta fitar, ta bayyana cewa Masarautar Saudi Arabia ta rufe bayar da bizar Hajji a hukumance tun ranar 1 ga Shawwal 1447AH, wanda ya yi daidai da 20 ga Maris, 2026.
Hukumar ta ce ta samar da biza ga dukkan maniyyatan da suka cika sharuddan rajista kafin wa’adin da aka gindaya.
NAHCON ta nuna damuwa kan yadda wasu ‘yan damfara ke amfani da kafafen sada zumunta na bogi da kuma kamfanonin tafiye-tafiye marasa izini wajen yaudarar jama’a da alkawarin samar da “tabbatacciyar bizar Hajji.”
Sanarwar ta kara da cewa hukumomin Saudiyya ba wai sun rufe bayar da bizar Hajji kadai ba, har ma sun dakatar da wasu nau’ikan biza na wucin gadi kamar ta yawon bude ido, ta aiki da kuma ta ziyartar iyali.
Hukumar ta jaddada cewa ba za a iya gudanar da aikin Hajji da irin wadannan biza ba, tana mai cewa sahihin izinin da ake bukata shi ne takardar izinin Hajji da ake samu ta hanyoyin hukuma kadai.
Ta kuma yi gargadin cewa duk wanda aka samu yana aikin Hajji ba tare da sahihin izini ba zai fuskanci hukunci mai tsanani daga hukumomin Saudiyya, ciki har da daurin watanni shida a gidan yari, tara har Riyal dubu 20 na Saudiyya, kimanin Naira miliyan 8.15, da kuma kora daga kasar tare da hana shi komawa na tsawon shekaru 10.
NAHCON ta bukaci jama’a su rika neman bayanai ne kawai ta hannun hukumar da kuma Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihohi, tana mai karin haske cewa ana yin dukkan rajistar Hajji ne ta hanyar dandalin Nusuk na hukuma.
A karshe, hukumar ta gargadi jama’a da su guji biyan kudi ga duk wani mutum ko hukuma da ke alkawarin samar da bizar Hajji ta barauniyar hanya, tare da bukatar a rika kai rahoton duk wani yunkurin damfara ga hukumomin tsaro da abin ya shafa

