Hukumar kula da aikin Hajji ta ƙasa (NAHCON) ta gudanar da ziyarar duba sansanin alhazai na Jihar Bauchi, a wani ɓangare na shirye-shiryen tabbatar da gudanar da Hajjin 2026 cikin tsari da nasara.
Yayin ziyarar, jami’in kula da jihohi da shiyyar Arewa maso Gabas na NAHCON, Alhaji Ahmed Muhammad Shira, ya bayyana cewa manufar duba sansanin ita ce tantance ingancin kayayyakin more rayuwa da kuma shirye-shiryen da aka yi domin karɓar maniyyata.
Ya yabawa Gwamnatin Jihar Bauchi bisa haɗin gwiwar da take yi da Hukumar Jin Daɗin Alhazai wajen bunƙasa sansanin, yana mai cewa wurin zai taka muhimmiyar rawa wajen horas da maniyyata kan yadda ake gudanar da ibadar Hajji.
Ahmed Shira ya ƙara da cewa, idan aka kwatanta da wasu sansanonin alhazai da ya ziyarta a wasu jihohi, sansanin na Bauchi ya zarce saboda ingantattun gine-gine da kayayyakin more rayuwa na zamani, ciki har da asibiti da sauran muhimman abubuwa da ke tallafawa jin daɗin maniyyata.
Haka kuma, ya yaba wa Gwamna Bala Mohammed bisa ƙoƙarinsa na inganta harkokin Hajji a jihar, tare da kira ga Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta jihar da ta tabbatar da kula da kayayyakin da aka samar yadda ya kamata.
A nasa jawabin, Sakataren Zartarwa na Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Bauchi, Dakta Imam Abdurrahman Ibrahim Idris, ya gode wa NAHCON bisa ziyarar.
Ya bayyana cewa wannan duba sansani na daga cikin matakan tabbatar da cewa dukkan shirye-shirye sun yi daidai da ƙa’idojin da aka shimfiɗa domin Hajjin 2026, musamman waɗanda hukumomin Saudiyya suka gindaya.
Haka kuma ya jaddada cewa hukumar na da ƙudurin bin ƙa’idojin ƙasa da ƙasa domin tabbatar da gudanar da Hajji cikin nasara ba tare da wata matsala ba.
Daga ƙarshe, ya buƙaci maniyyata da su yi amfani da kayayyakin da ke sansanin yadda ya kamata, tare da kiyaye dokoki da tsare-tsare domin amfanin su da kuma na waɗanda za su zo nan gaba.
Wannan ziyara na daga cikin rangadin da NAHCON ke yi a faɗin ƙasa domin tantance shirye-shiryen Hajji yayin da ake ƙara ƙaimi gabanin kakar Hajjin 2026.

