Hukumar Kula da Ayyukan Hajji ta Ƙasa (NAHCON) ta kai ziyarar duba aiki a sansanin wucewar alhazai na Jihar Kaduna da ke Mando domin tantance shirye-shiryen Hajjin 2026.
KARANTA LABARI MAKAMANCIN WANNAN : Hukumar Alhazai Ta Kaduna Ta Fara Mayar Da Kudade Ga Alhazan Da Suka Halarci Aikin Hajin 2023
Tawagar, ƙarƙashin jagorancin Sheikh Muhammad Bin Othman, ta bayyana gamsuwa da irin gagarumin sauyi da aka samu a sansanin, inda ta yaba da jagorancin Hukumar Alhazai ta Jihar Kaduna karkashin Malam Salihu S. Abubakar.
NAHCON ta ce ayyukan da aka aiwatar, ciki har da gina hanyoyi, girke fitilun hasken rana, sabon ɗakin tarba, cibiyar ICT da kasuwa ta zamani, sun nuna ƙwazo da kyakkyawan tsari.
Haka kuma, ta yaba wa Gwamnan Jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, bisa goyon bayan da yake bai wa hukumar, tare da kira ga sauran jihohi su yi koyi da irin wannan ci gaba.
A nasa bangaren, Sakataren Gudanarwa na Hukumar, Malam Baba Rufa’i, ya danganta nasarorin da aka samu da haɗin kai da goyon bayan gwamnati.
Ziyarar ta tabbatar da Kaduna a matsayin abin koyi wajen shirye-shiryen Hajji a Nijeriya.

