Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Kaduna ta gudanar da ziyarar wayar da kai a Ƙaramar Hukumar Kauru a matsayin wani ɓangare na ci gaba da yaƙin neman wayar da kan masu niyyar zuwa aikin Hajjin shekarar 2027, tare da ƙarfafa su su yi rajista kafin wa’adin rufe rajista na ranar 26 ga Satumba, 2026.
A cewar Jami’in Hulda da jama’a na Hukumar, Ibrahim Datti, tawagar ta samu jagorancin Shugaban Hukumar, Malam Salihu S. Abubakar, tare da Sakataren Gudanarwa na Hukumar, Malam Baba Rufa’i, mambobin gudanarwar Hukumar da kuma ɗaya daga cikin mambobin Kwamitin Musamman na Hajji na Jihar Kaduna, Imam Buhari Maraban.
Da yake jawabi ga mahalarta taron, Shugaban Hukumar ya yi kira ga al’ummar Kauru da sauran mazauna Jihar Kaduna da su yi amfani da sauran lokacin rajista wajen biyan kuɗin Hajji ta hannun Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Kaduna.
Malam Salihu S. Abubakar ya bayyana cewa Hukumar ta samu gagarumin ci gaba wajen inganta ayyukanta, musamman ta hanyar sabunta Sansanin Alhazai na Mando zuwa matakin ƙasa da ƙasa, tare da ɗaukar wasu matakan da za su ƙara inganta jin daɗi da walwalar alhazan jihar a Ƙasar Saudiyya.
Ya kuma yaba da jajircewar Gwamnan Jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, bisa ci gaba da ba da goyon baya wajen inganta gudanar da aikin Hajji da walwalar alhazan jihar.
Haka kuma ya roƙi masu niyyar zuwa Hajji da kada su jira zuwa lokacin ƙarshe kafin su kammala rajistarsu, sai dai su yi hakan kafin wa’adin da aka ƙayyade.
A nasa jawabin, Sarkin Kauru, Alhaji Zakari Ya’u Usman, ya nuna godiyarsa ga shugabannin Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Kaduna bisa kai wannan shirin wayar da kai zuwa masarautarsa. Ya kuma ƙarfafa masu niyyar zuwa Hajji daga Ƙaramar Hukumar Kauru da su yi rajista tare da biyan kuɗin Hajji ta Cibiyar Rajistar Alhazai ta Ƙaramar Hukumar Kauru, domin tabbatar da samun damar halartar aikin Hajjin shekarar 2027.

