…An Nada Sarkin Karaye a Matsayin Mataimakin Amirul Hajj…
Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya amince da naɗin Sarkin Gaya, Mai Martaba Alhaji Dakta Aliyu Ibrahim Abdulkadir, a matsayin Amirul Hajj na aikin Hajjin shekarar 2026.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar ranar Talata.
Haka kuma, an nada Sarkin Karaye, Mai Martaba Alhaji Muhammad Muhammad Maharaz, a matsayin Mataimakin Amirul Hajj.
Sanarwar ta ƙara da cewa ana sa ran Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Kano za ta bai wa Amirul Hajj da mataimakinsa cikakken goyon baya domin tabbatar da gudanar da aikin Hajji cikin nasara da kwanciyar hankali.
Gwamnatin ta kuma yi wa Amirul Hajj, mataimakinsa, shugabanni da ma’aikatan Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Kano fatan alheri tare da addu’ar Allah Ya sa aikin Hajjin ya gudana cikin nasara, Ya kuma karɓi ibadun alhazan tare da dawo da su gida lafiya.

