Eusoff Azman daga Cheras, Kuala Lumpur, ya bayyana matuƙar godiya bayan an zaɓe shi domin gudanar da aikin Hajjin shekarar 2026, inda ya danganta hakan da shirin dogon lokaci da sadaukarwar mahaifiyarsa.
Duk da cewa ya yi tafiyar shi kaɗai ba tare da ‘yan uwansa ba, tsofaffin alhazai sun nuna masa kulawa da ƙauna a duk tsawon zamansa.
An zaɓi Eusoff Azman domin aikin Hajjin 2026.
Mahaifiyarsa ta yi masa rijista da Lembaga Tabung Haji tun a shekarar 2008, inda ta riƙa tara masa kuɗi tsawon shekaru domin tabbatar da cewa wata rana zai samu damar zuwa aikin Hajji.
Ga Eusoff, wannan dama ta Hajjin bana ita ce sakamakon wani tsari da aka fara tun yana jariri.
Ya ce ba zai iya misalta irin godiyar da yake yi wa mahaifiyarsa ba saboda irin ƙoƙarin da ta yi da hangen nesa.
“Na gode Mama. Da ba ki fara tanadi da tsara min wannan tun ina ƙarami ba, da watakila ban samu wannan damar ba a yau,” in ji shi.
Eusoff ya ƙara da cewa, ainihin ma’anar sadaukarwar mahaifiyarsa ta bayyana gare shi ne bayan ya isa Makkah.
“Da na iso nan ne na fahimci cewa mahaifiyata ba kawai tana tunanin rayuwata ta duniya ba, tana kuma shirya ni ne domin lahira tun ina jariri,” in ji shi.
Eusoff, tsohon ɗalibin Royal Military College, ya bayyana aikin Hajji a matsayin ɗaya daga cikin mafi muhimmancin abubuwan da ya taɓa fuskanta a rayuwarsa. Wannan ne karo na farko da ya yi tafiya ƙasashen waje ba tare da iyalinsa ba.
Ya ce iyayensa da wasu daga cikin ‘yan uwansa sun riga sun sauke farali, kuma a wannan shekarar ne nasa lokacin ya zo.
Duk da cewa ya zo shi kaɗai, Eusoff ya ce bai taɓa jin kaɗaici ba. Tsofaffin alhazai da ke tare da shi sun riƙa kula da shi kamar ɗansu.
“Ni ne ƙarami a cikin
ƙungiyarmu. Abokan ɗakina duk suna cikin shekarun 50 zuwa 60, amma suna ɗaukar ni kamar ɗansu. Kullum suna tambayata ko na ci abinci ko na dawo ɗaki lafiya,” in ji shi.
“A nan, ba wai ibada kaɗai nake koya ba, har da darussan rayuwa, girmama manya, da kuma ma’anar ‘yan uwantaka,” ya ƙara da cewa.
Eusoff ya ce yanzu ya fahimci irin sadaukarwar shiru da iyayensa suka yi tsawon shekaru, suna tara kuɗi kaɗan-kaɗan domin ya samu damar zuwa Hajji wata rana.
Ya kuma yi fatan cewa iyaye za su samu ƙwarin gwiwa su fara shirya irin wannan dama tun da wuri ga ‘ya’yansu.
(II)

