Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Kano na sanar da dukkan maniyyata aikin Hajjin bana da kuma al’umma baki ɗaya cewa kamfanin jirgin sama na Max Air ya sauya ranar tashin jirgin da aka tsara domin jigilar alhazan Kano zuwa Ƙasar Saudiyya domin gudanar da aikin Hajjin shekarar 2026.
Za a tuna cewa an fara tsara tashin jirgin farko ne a ranar Alhamis, 14 ga watan Mayu, 2026. Sai dai sakamakon wasu sauye-sauye da aka samu a shirye-shiryen zirga-zirgar jirage, yanzu za a gudanar da tashin farko ne a ranar Juma’a, 15 ga watan Mayu, 2026.
Alhazan da wannan sauyi ya shafa sun fito ne daga ƙananan hukumomi kamar haka:
Gwale
Dala
Fagge
Ungogo
Saboda haka, ana sanar da dukkan alhazan da aka tsara za su tashi a ranar 14 ga watan Mayu, 2026 daga waɗannan ƙananan hukumomi cewa an mayar da tashinsu zuwa ranar 15 ga watan Mayu, 2026.
Kamfanin Max Air na ba da haƙuri kan duk wata matsala da wannan sauyi ka iya haifarwa, tare da godiya bisa fahimta da haɗin kan maniyyata.
Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Kano tana tabbatar wa da dukkan alhazai cewa ana ci gaba da ɗaukar matakan da suka dace domin tabbatar da jigilar alhazai cikin nasara da kwanciyar hankali. Haka kuma, hukumar za ta ci gaba da sanar da duk wasu sababbin bayanai da jadawalin lokacin kai rahoto ga alhazai yadda ya kamata.

