Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Sakkwato ta samu nasarar kammala shirin wayar da kai da ilmantar da maniyyatan aikin Hajji gabanin fara gudanar da aikin na bana.
Kamar yadda Shugaban sashen yada labarai da sadarwa na Hukumar, Faruku Umar ya sanar, an gudanar da shirin ne a Cibiyar nazarin Alqurani ta Sultan Maccido, inda ya haɗa da mahalarta daga ƙananan hukumomin Sakkwato ta Arewa da Sakkwato ta Kudu, da kuma maniyyatan da suka biya ta hedikwatar Hukumar (PWA) da kuma jami’an gwamnatin jiha (SGO).
A wajen rufe shirin, manyan malamai da jami’an Hajji sun gabatar da cikakkun darussa da shawarwari masu amfani kan muhimman rukunnan Hajji.
Haka kuma, an yi bayani kan sabbin tsare-tsare da ƙa’idoji da aka ƙaddamar domin tabbatar da cewa maniyyata sun samu isasshen shiri don gudanar da Hajji cikin sauƙi da kwanciyar hankali tare da samun lada.
Hukumar ta sake jaddada kudurinta na ci gaba da wayar da kai da tallafawa dukkan maniyyatan Jihar Sakkwato, tare da ƙarfafa su da su bi dukkan ƙa’idojin Hajji domin samun nasarar gudanar da ibadar.

