Hukumar Alhazai ta Kasa, NAHCON, ta ƙaddamar da sabuwar cibiyar karɓar ƙorafe-ƙorafen alhazai ta zamani domin inganta sadarwa da kula da jin daɗin alhazan Najeriya yayin gudanar da aikin Hajjin 2026.
Shugaban cibiyar karɓar ƙorafe-ƙorafen, Shehu Raji, ne ya bayyana hakan yayin da yake yi wa manema labarai jawabi a cibiyar da ke Ummuljud a birnin Makkah na ƙasar Saudiyya.
Ya ce sabon tsarin ya bambanta da tsohon tsarin analog da hukumar ke amfani da shi a baya, inda mutum ɗaya kacal ake iya amsa kiransa a lokaci guda. A cewarsa, sabuwar fasahar Cloud da aka samar za ta ba da damar karɓar kira da dama lokaci guda ta hanyar amfani da lamba ɗaya.
Shehu Raji ya bayyana cewa kasancewar Najeriya na da sama da alhazai dubu hamsin a aikin Hajji, sabon tsarin zai taimaka wajen sauƙaƙa sadarwa tare da gaggauta magance matsaloli da ƙorafe-ƙorafen alhazai.
Ya ƙara da cewa cibiyar tana aiki sa’o’i ashirin da huɗu a kullum, kuma tana da alaƙa da sassa daban-daban da hukumomin da ke kula da jin daɗin alhazai a Masarautar Saudiyya.
A cewarsa, duk wata ƙorafi da ta shafi masauki, abinci, lafiya, tsaro ko harkokin jakadanci ana miƙa ta ga hukumomin da suka dace domin ɗaukar matakin gaggawa
Shugaban cibiyar ya kuma bayyana cewa an samar da kundin bayanai da ke ɗauke da lambobin waya da hanyoyin sadarwa na jami’an Najeriya da ke gudanar da aikin Hajji domin tabbatar da haɗin kai da saurin bayar da amsa.
Ya ce wannan sabon tsarin ya yi daidai da manufofin Vision 2030 na Saudiyya da kuma ƙoƙarin Najeriya na amfani da fasahar zamani wajen gudanar da harkokin Hajji.
Shehu Raji ya buƙaci alhazan Najeriya da su riƙa amfani da cibiyar wajen kai rahoton matsalolinsu na gaskiya, yana mai cewa ƙorafe-ƙorafen da ake samu za su taimaka wajen tantance ayyukan kamfanonin masauki, abinci da sauran masu bayar da hidima a nan gaba.
Haka kuma ya yi kira ga jama’a da su guji yaɗa ƙarya da jita-jita da ka iya haddasa firgici a tsakanin alhazai.
NAHCON ta ce ƙaddamar da wannan cibiyar na daga cikin matakan da take ɗauka domin tabbatar da ingantaccen kula da jin daɗin alhazai da bunƙasa sadarwa a duk tsawon aikin Hajjin 2026.

