Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Kano ta sanar da cewa za ta fara jigilar rukuni na farko na maniyyatan jihar zuwa ƙasar Saudiyya a ranar 14 ga Mayu, 2026, wanda zai zama farkon gudanar da ayyukan Hajjin bana.
A cewar Jami’in hulda da jama’a na Hukumar Sulaiman Abdullahi Dederi, Darakta Janar na Hukumar, Alhaji Abubakar Ibrahim Matawalle, ne ya bayyana hakan yayin bikin rufe Bitar Alhazai da aka gudanar a Makarantar Nazarin Larabci da ke Kano.
Ya ce wannan rana ta yi daidai da jadawalin da National Hajj Commission of Nigeria ta fitar, inda aka zaɓi kamfanin jirgin sama na Max Air domin gudanar da jigilar.
Ya ƙara da cewa Hukumar ta kammala dukkan shirye-shiryen da suka dace tun da wuri domin tabbatar da fara aikin cikin tsari da nasara.
A nasa jawabin, Shugaban Hukumar, Alhaji Yusuf Lawan, ya buƙaci maniyyata su riƙa duba littattafan horon Hajji akai-akai a gidajensu domin ƙara fahimtar ibadun Hajji da yadda ake gudanar da su yadda ya kamata.
Haka kuma ya shawarce su da su bi dokoki da ƙa’idojin da hukumomin Najeriya da na Saudiyya suka shimfiɗa domin samun ingantaccen gudanar da Hajji ba tare da wata matsala ba.
A wajen taron, wasu hukumomin tsaro da abokan hulɗa da ke da hannu a harkokin Hajji sun gabatar da jawaban nasu, ciki har da Hukumar Shige da Fice ta Najeriya, NDLEA, Kotun Hajji, NOA, Max Air da Hisbah.

